Wasu rahotanni na cewa, kasashen Sin da Rasha sun raba daftarin labari kan daidaita batun zirin Koriya a siyasance, a tsakanin kasashe mambobin kwamitin sulhu na MDD.
Game da hakan, a Jumma'ar nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya tabbatar da wannan labari, yana mai cewa, sakamakon kyakkyawan ci gaba da aka samu a zirin Koriya a kwanan baya, ya sa ya kamata kwamitin sulhun ya nuna alamar kara azama da goyon baya a fannin yin tattaunawa da shawarwari. (Tasallah Yuan)