in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar Rodong Simun: Ziyarar da Kim Jong-un ya yi a kasar Sin ta nuna niyyar Koriya ta Arewa ta kara kyautata huldar dake tsakaninta da Sin
2018-03-30 13:21:46 cri
Jaridar "Rodong Simun" mallakar jam'iyya mai mulkin kasar Koriya ta Arewa ta KWP, ta wallafa wani bayani a jiya, wanda mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar KWP Choe Hwi ya rubuta, inda ya ce, kwarya-kwaryar ziyarar da shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar KWP, Kim Jong-un ya yi a kasar Sin, na da ma'ana sosai ga tarihi, wadda ta nuna yadda kasar Koriya ta Arewa ke da niyyar kara kyautata huldar dake tsakanin ta da kasar Sin.

Babban jami'in kasar Koriya ta Arewa ya rubuta cewa, kasashen Koriya ta Arewa da Sin sun kulla zumunci ne tun lokacin da suka yi kokarin wanzar da tsarin siyasa na gurguzu a kasashensu, wanda bai taba canzawa ba. A cewarsa, jam'iyyar KWP da gwamnatin kasar Koriya ta Arewa suna da cikakkiyar niyyar ci gaba da kokarin kyautata huldar dake tsakaninsu da kasar Sin. Ya ce wannan manufa ita ce dalilin da ya sa Kim Jong-un ya kawo ziyara kasar Sin a wannan karo.

Cikin bayaninsa, jami'in kasar Koriya ta Arewa ya waiwayi yadda aka sada zumunci tsakanin Koriya ta Arewa da kasar Sin a baya, inda ya ce wannan zumunci wani gado ne mai daraja matuka da mazan jiyan kasashen 2 suka bar wa mutanen wannan zamani. A cewarsa, don tabbatar da samun adalci da zaman lafiya, da neman wanzar da tsarin gurguzu, kasashen Koriya ta Arewa da Sin, sun yi kokarin hada gwiwa da juna, inda jama'ar kasashen 2 da yawa suka sadaukar da rayukansu, don neman baiwa daukacin al'ummomin kasashen 2 zaman rayuwa mai walwala gami da makoma mai haske. Wannan hadin gwiwa, a cewar jami'in kasar Koriya ta Arewa, ta na da daraja sosai.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China