in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin shirya ganawa tsakanin shugabannin Koriya ta Arewa da ta kudu ya kira taro karo na farko
2018-03-17 11:17:23 cri
Kwamitin shirya ganawa tsakanin shugabannin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu, ya kira taro karo na farko, domin yin bayani kan ganawar da shugabannin kasashen biyu da za su yi a karshen watan nan na Maris.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Koriya ta Kudu ta fitar a jiya ya ruwaito cewa, kwamitin zai kuma samar da wata tawagar masu bada shawara da za ta kunshi mutane 30 zuwa 40, inda tsohon Ministan harkokin hadin kai na Koriya ta Kudu Lim Dong-won zai shugabanci tawagar, domin kara wa juna sani kan ganawa sau biyu da shugabannin kasashen biyu suka taba yi a baya, tare kuma da tattara shawarwari daga bangarori daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China