Lu Kang, ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su nuna goyon baya ga bangarorin biyu, ta yadda za su kyautata dangantakar dake tsakaninsu, da kuma ciyar da shawarwarin neman sulhu a tsakaninsu gaba.
Bisa labarin da aka samu, an ce, cikin shawarwarin da bangarorin biyu suka yi a yau Alhamis, sun tsai da kudurin ganawa a tsakanin shugabannin kasashen biyu a Gidan Zaman Lafiya dake birnin Panmunjom a ranar 27 ga watan Afrilu mai zuwa. (Maryam)