Haka kuma, an nuna yabo ga tawagar domin babbar gudummawa da ta bayar kan goyon bayan kasar Somaliya wajen neman sulhu da shimfida zaman lafiya, da warware sabani da kuma ba da taimako a yayin babban zaben kasar. A sa'i daya kuma, kwamitin ya sake jaddada girmamawarsa kan 'yancin kan kasar Somaliya da kuma cikakken zaman kasar, ya kuma bayyana muhimmiyar ma'ana ta hana yaduwar rikice-rikicen a yankunan kasar ta Somaliya.
An kafa tawagar bada taimako ga kasar Somaliya ne a watan Yuni na shekarar 2013, bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lambar 2102. (Maryam)