in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen da suka rasu sakamakon fashewar bom a Somaliya sun karu zuwa 32
2018-02-25 12:51:26 cri
An samu labari daga hukumomin tsaron kasar Somaliya a jiya ranar Asabar cewa, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bom da aka ajiye a mota har sau biyu a Mogadishu, babban birnin kasar ya karu zuwa 32.

An ce, a ranar 23 ga wata da yamma misalin karfe 6, wata motar dakaru masu makamai da aka ajiye bom ta fashe a wurin dake dab da hedkwatar hukumar lekan asiri da tsaro ta kasar Somaliya. Bayan minti 15, an tayar da bom da aka ajiye a motar dake kan hanyar zuwa fadar shugaba a wata unguwar dake kusa da fadar. An ji babbar murya ce sakamakon fashewar bom sau biyu.

Bisa kididdigar da masu aikin ba da agaji suna yi, an ce, fashewar bom din har sau biyu sun haddasa rasuwar mutane a kalla 18, tare da rautata mutane 20, yanzu masu jin rauni na samun jinya ne a asibitocin dake Mogadishu.

Mazauna wurin dun bayyana wa kafofin watsa labaru cewa, bayan an samu fashewar bom a fadar shugaba, an yi musayar wuta sosai a tsakanin sojojin tsaron kasa da dakaru masu makamai.

A cewar hukumomin tsaron kasar, dakaru 5 sun rasu, wani mai aikin tsaron kasar ma ya mutu .

Kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya ce ta sanar da tayar da harin da ya faru a ranar 23 ga wata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China