in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan AU a Somaliya ya yi kira da a kara azama wajen yaki da Al-Shabab
2018-03-14 10:20:43 cri
Babban wakilin kungiyar hadin kan Afirka ta AU a Somaliya, kuma jagoran rundunar AMISOM dake kasar Francisco Madeira, ya yi kira ga gwamnatocin yankuna dake kasar, da su kara zage damtse wajen yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabab.

Francisco Madeira, wanda ke wakiltar shugaban hukumar zartaswar AU a Somalia, ya yi wannan kira ne yayin zantawar sa da shugaban gwamnatin yankin HirShabelle Mohamed Abdi Waare, game da batun shirin da ake yi na mika aikin tsaron yankunan Somaliya hannun gwamnatin kasar. Mr. Madeira ya ce akwai bukatar gaggawa ta ganin Somalia ta sake farfadowa.

Kaza lika jami'in ya bayyana cewa, yana sane da irin kalubalen da yankin na HirShabelle ke fuskanta, kasancewar sa yanki na baya bayan nan da aka kirkira a kasar ta Somaliya.

Ya ce rundunar AMISOM za ta ci gaba da hadin gwiwa da gwamnatocin yankunan kasar, wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana, da salon mulki na gari, a daukacin yankunan da ta 'yantar.

Ganawar jami'an biyu dai ta biyo bayan harin da mayakan Al-Shabab suka kai wa tawagar jami'an AMISOM, wadanda ke rakiyar wasu motocin agajin jin kai tsakanin birnin Mogadishu zuwa Jowhar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China