in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a kara taimakawa shirin Aamin dake agazawa marasa lafiya kyauta a Somaliya
2018-02-06 20:08:00 cri
Manzon musammam na MDD dake Somaliya Micheal Keating ya yi kira da a kara taimakawa shirin motocin dake kai daukin gaggawa kyauta ga mazauna Somaliya wato Aamin

Jami'in wanda har ila shi ne mataimakin babban sakataren MDD dake Somaliya, ya kuma yaba da shirin motocin kai dauki kyauta na Aamin, wanda ke gudanar da irin wadannan ayyuka ba dare ba rana a shekara.

Wata sanarwa da ya fitar ta hannun tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya (UNSOM) a jiya Litinin da yamma, Keating ya yi kira da a kara taimakawa shirin kai daukin gaggawar wanda ke aiki da motocin daukar marasa lafiya guda 10, da cibiyoyin kula da marasa lafiya na tafi da gidanta, da wuraren kai agaji ta yadda za su tunkari duk wani kalubale da ka iya kunno kai a babban birnin kasar cikin dan kankanin lokaci.

Aikin na Aamin dai ya janyo hankalin kasashen duniya, tun bayan da wani bam da ya tashi cikin wata mota ranar 14 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata a Mogadishu, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane a kalla 512 kana sama da mutane 300 kuma suka jikkata, kuma ma'aikatan dake gudanar da wannan shiri su ne na farko da suka bayyana a wajen da lamarin ya faru. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China