in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin wanzar da zaman lafiyar AU ya horas da jami'an 'yan sanda na Somaliya game da kare hakkin dan adam
2018-03-25 13:03:06 cri
Shirin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM) a ranar Asabar ya kammala wani shirin wayar da kai game da kaucewa nuna bambancin jinsi inda ya horas da jami'an 'yan sanda kimanin 98 a wasu shiyyoyin jihohin kasar Somaliya 4 domin taimaka musu wajen fadada ilminsu game da batutuwan da suka shafi kare hakkin dan adam.

Shirin na AU ya bayyana cewa, jami'an da aka baiwa horon sun hada da sauran jami'an tsaro daga yankunan Kismayo, Baidoa, Beletweyne, da kuma wanda aka gudanar na kwanan nan a yankin Adado dake tsakiyar Somaliya.

Stella Maranga, jami'ar kula da sashen yaki da nuna bambancin jinsi ta shirin na AMISOM ta bayyana cewa, makasudin shirin bada horon shi ne domin wayar da kan dakarun sojin da sauran jami'an tsaro don su fahimci muhimmancin kawar da bambancin jinsi da kuma mutunta hakkin dan adam.

Maranga ta ce, an shirya taron ne domin a bayyana wasu muhimman batutuwa da suka shafi batun kawar da nuna bambancin jinsi, domin baiwa ko wane bangare damar shiga a dama da shi a dukkan al'amurran harkokin yau da kullum.

AMISOM ya sanar da cewa, shirin bada horon yana daya daga cikin manufar shirin na kiyaye zaman lafiyar wajen wayar da kan jami'an tsaron Somaliya, domin su samu damar aiwatar da ayyukansu bisa doka da oda.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China