Gwamnatin kasar Somaliya ta tabbatar a jiya Litinin cewa, sojojin gwamnatin kasar sun gwabza wani kazamin fada da dakarun kungiyar al-Shabaab a jihar Bay dake kudancin kasar, lamarin da ya kai ga kashe mayakan kungiyar a kalla 7, tare da raunata wasu, yayin da sojojin gwamnati kuma 4 suka rasa rayuka, ciki har da wani babban hafsa.
Kungiyar al-Shabaab wata kungiya ce ta masu tsattsauran ra'ayi, wadda ke da alaka da kungiyar al-Qaeda. A shekarun nan, dakarun al-Shabaab sun yi ta kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasar Somaliya da makwabtanta.(Bello Wang)