in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somalia da MDD sun kaddamar da shirin inganta rayuwar 'yan gudun hijira
2018-02-01 09:41:23 cri
A jiya Laraba Somaliya da MDD suka kaddamar da wani shirin na musamman na hadin gwiwa inda suka nemi shawarwari daga matasan kasar ta Somaliya game da irin hanyoyi da ya dace a bi don inganta rayuwar mutanen dake zaune a sansanin 'yan gudun hijira a kasar.

Dukkan jami'an na bangarorin biyu wato bangaren gwamnatin Somalia da na MDD wadanda suka halarci bikin kaddamar da shirin a Mogadishu, sun bukaci matasan Somalia da su gabatar musu da dabarun da suke ganin idan aka yi amfani da su za'a iya magance dundun matsalolin da mazauna sansanonin 'yan gudun hijirar ke fuskanta.

Achim Steiner, jami'in shirin raya ci gaban na MDD (UNDP), ya shawarci matasan da su tsara wani shirin hadin gwiwa domin samar da dabarun da suka dace.

Cikin wata sanarwar da ofishin kula da shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a UNSOM ya fitar, ya ce, sun sha gudanar da ayyukan samar da agajin gaggawa, amma abin da suke so shi ne yin aiki tare da matasan domin samun nasarar kaiwa kasar Somaliya zuwa mataki na gaba.

Wannan shiri dai shi ne irinsa na uku, kuma sabon shirin na wannan karo an samar da shi ne saboda matasa 'yan Somali dake rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira, da 'yan gudun hijirar da suka koma gidajensu, da kuma matasan dake yankunan da suka karbi bakuncin 'yan gudun hijirar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China