in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a karfafa ci gaba a yankin tabkin Chadi don inganta zaman lafiya
2018-03-23 12:48:27 cri

Mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina Mohammed, ta yi kira da a kara kokarin samun kwanciyar hankali a yankin tafkin Chadi ta hanyar raya shi, la'akari da nasarorin da aka samu a yaki da kungiyar Boko Haram.

Amin Mohammed ta shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, ayyukan dakarun kawance na kasashe daban-daban, sun taimaka wajen kwato mutanen da aka yi garkuwa da su da yankunan da aka mamaye, tana mai cewa, yanzu lokaci ne mai muhimmanci na tabbatar da kwanciyar hankali a yankunan da aka kwato tare da raya su.

Ta ce, matakan tsaro da na soji sun kai iyakarsu, inda ta ce, babu yadda za a samu zaman lafiya ba tare da dawwamamiyar ci gaba ba, haka zalika amfana daga ci gaba za ta kasance cikin hadari matuka idan babu zaman lafiya mai dorewa.

Ta kara da cewa, Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare da kunar bakin wake da satar mutane, kamar yadda suka yi cikin watan da ya gabata, inda suka sace 'yan mata sama da 100 da aka sako a baya-bayan nan, a yankin arewa maso gabashin kasar Nijeriya.

Har ila yau, ta ce MDD na mara baya ga kungiyar tarayyar Afrika da kwamitin raya yankin tafkin Chadi a kokarinsu na samar da wani shiri na samun kwanciyar hankali da fafadowa ga yankin, wanda za a kaddamar a wata mai zuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China