in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya bukaci a nuna fahimtar juna da hakuri
2018-03-21 13:38:02 cri
Jiya Talata, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya gabatar da jawabi a cikakken zaman taron tunawa da ranar kawar da wariyar launun fata ta MDD, inda ya bukaci al'ummar duniya su nuna fahimtar juna a tsakaninsu, kana su kawar da duk wani batu na nuna bambance bambancen dake tsakanin mutane daban daban na duniya.

Cikin jawabinsa, Mr. Guterres ya yi kira ga mutanen kasa da kasa da su hana yaduwar tsattsauran ra'ayoyi, kuma su dakatar da yin amfani da kalmomin nuna kiyayya. Haka kuma, bai kamata a nuna kiyayya kan wani ko wata ba saboda bambancin addini, ko launin fata ko kuma nuna kyama ga matsayi da bil adama ya zabawa kansa don biyan sha'awarsa ta jima'i da dai sauransu.

Daga bisani kuma, ya bukaci a nuna kiyayya kan wasu shugabannin kasa da kasa wadanda suke yada bayanai game da wariyar launin fata, da bata sunan 'yan ci rani da mutanen ketare.

Babban taron MDD ya mai da ranar 21 ga watan Maris ta kowace shekara, a matsayin ranar kawar da wariyar launin fata ta duniya, sabo da a ranar 21 ga watan Maris ta shekarar 1960 ne, mutane masu dimbin yawa suka rasa rayukansu sakamakon harin da gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta kai musu, a yayin da suka yi zanga-zanga mai taken "kin manufar wariyar launin fata" a garin Sharpeville na kasar, lamarin da ya sosa ran al'ummomin kasa da kasa kware da gaske.

Mr. Guterres ya ce, manufar wariyar launin fata da wadanda aka kashe a garin Sharpeville suka nuna adawa, ta nuna amincewar gwamnati ta lokacin kan wannan lamari. Amma abin bakin ciki shi ne, ya zuwa yanzu, ba a iya kawar da wariyar launin fata da nuna kiyayya ga 'yan cin rani da mutanen ketare da dai sauran tsattsauran ra'ayoyi a duk fadin duniya baki daya ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China