Sakamakon irin muhimmancin da take bayarwa ga sauye-sauyen na UPR, kasar Sin ta bayyana cewa yin hadin gwiwa abu ne mai matukar muhimmanci da zai taimaka wajen aiwatar da shawarwarin da za su taimakawa kasashen duniya masu tasowa, in ji jami'in diplomasiyyar na Sin.
Da yammacin ranar Litinin ne kwamitin kare hakkin bil adama na MDD ya gudanar da babbar muhawara game da yin sauye-sauye a tsarin na UPR, inda masu gabatar da kasidu suka nuna cewa yin gyare-gyaren wata babbar nasara ce, kasancewar batu ne da ya shafi aiwatar da tsarin a aikace, kana ya kasance a matsayin wata dama ta yin tsokaci kan irin nasarorin da aka cimma da kuma kalubalolin da dukkan kasashe ke fuskanta wajen aiwatar da muhimman batutuwan da suka shafi kare hakkin dan adam.
Mafi yawan kasashen duniya sun rungumi tsarin na UPR, kasancewarsa wani tsari ne da ake sake yin nazari kansa a duk bayan shekaru 4, don nazartar yanayin halin da hakkin dan adam ke ciki, da nazartar al'amurra da suka shafi wannan batu, da sanya ido kan irin nasarorin da kasashen duniya suka cimma a wannan fanni. (Ahmad Fagam)