Kwamitin MDDr yana la'akari da daftarin wanda kasashen Kuwait da Sweden suka tsara, wanda ya bukaci a tsagaita bude wuta daga dukkanin bangarorin dake yaki da juna a duk fadin kasar ta Syria in banda dakarun sojin dake yakar kungiyar IS, da al Qaeda da al Nusra Front, har na tsawon kwanaki 30 domin a samu damar shigar da kayayyakin jin kai da masu ba da agajin kiwon lafiya a yankunan kasar.
Jakadan kasar Sweden a MDD Olof Skoog, ya bayyana cewa, yana fata kwamitin sulhun MDDr zai kada kuri'a kan kudurin a ranar Alhamis. Sai dai jakadan kasar Rasha a MDDr Vassily Nebenzia ya ce, yana fata za'a yi wasu gyare gyare kan kudurin domin ya kasance mai inganci.
A cewar Nebenzia, babu wata matsaya da aka cimma a zaman kwamitin game da batun tsagaita bude wuta, a yayin da tashin hankali ke sake tsakananta a kasar sakamakon karuwar kaddamar da hare hare daga 'yan ta'adda.(Ahmad Fagam)