Ana zargin dakaru 'yan ta'adda na Boko Haram da sace 'yan matan. Cikin jawabin Antonio Guterres da aka gabatar ta bakin kakakinsa, Stephane Dujarric, babban sakataren ya kalubalanci wadanda suka aikata wannan zamba da su saki dukkan 'yan matan da aka sace ba tare da gindaya wani sharadi ba, sa'an nan a ba su damar komawa gidajensu lami lafiya.
Ban da haka kuma, babban sakataren MDD ya bukaci hukumomi daban daban na Najeriya da su yi kokarin gurfanar da wadanda suka saci 'yan matan a gaban kotu.(Bello Wang)