in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfafawa mata shi ne babban buri na neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030
2018-03-09 10:00:48 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya yi gargadi kan illar da za a iya yi wa al'ummomin kasa da kasa, sabo da nuna wariya da rashin girmama mata.

Antonio Guteress wanda ya bayyana haka a jiya, yayin da yake jawabi domin ranar mata ta duniya, ya kuma jaddada cewa, karfafawa mata shi ne babban burin jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030.

Bugu da kari, ya ce tabbatar da adalci shi ne babban hakkin dan Adam. Yana mai cewa, a halin yanzu, cimma burin shimfida adalci a tsakanin jinsi daban da kuma karfafawa mata da 'yan mata su ne manyan ayyukan dake gaban al'ummomin kasa da kasa, kuma su ne babban kalubale ta fuskar hakkin dan Adam da ake fuskanta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China