in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya jadadda muhimmancin kare barkewar rikici
2018-02-22 09:42:01 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya jadadda muhimmancin da ke akwai na daukar managartan dabarun kare aukuwar rikici maimakon tunkararsa.

Da yake jawabi yayin muhawarar kwamitin sulhu na majalisar, kan manufofi da tsare-tsarensa na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, Antonio Guterres ya ce al'ummomin duniya na bata lokaci da kudi mai tarin yawa, wajen tunkarar rikice-rikice maimakon kare aukuwarsu. Ya na mai cewa kamata ya yi a sake daidaita dabarun wanzar da tsaro da zaman lafiya a duniya.

Ya ce kamata ya yi burinsu a majalisar, ya zama na yin dukkan mai yuwa wajen taimakawa kasashe kare barkewar rikice-rikice dake mummunan tasiri kan bil'adama. Inda ya ce ya kamata wannan buri ya fadada ya kai ga kare iftila'i da sauran matsaloli, baya ga yake-yake da rikici.

Antonio Guterres, ya ce kare aukuwar rikici hakki ne da ya rataya kacokan kan kasashe mambobin majalisar, inda ya tabbatar da cewa MDD za ta marawa kasashe baya, wajen warware takkadama tare da kare barkewar rikici.

Ya kuma karfafawa kasashen gwiwar amincewa da ikon kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC, ya na mai bukatarsu da su yi amfani da ita da sauran kotunan duniya wajen warware rikici tare da kare ta'azzararsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China