in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tattauna batun hakkin dan Adam a Falesdinu cikin taron MDD
2018-03-21 10:59:48 cri
An yi mahawara kan yanayin hakkin dan Adam a yankunan Falesdinu da wasu kasashen Larabawa, wadanda suke karkashin mallakar Isra'ila a halin yanzu, cikin taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 37 da aka yi jiya a birnin Geneva na tarayyar Switzerland. Mahalartar taron, sun nuna damuwarsu matuka, kan tabarbarewar yanayin hakkin dan Adam a yankunan da Isra'ila ta mallake, a sa'i daya kuma, sun yi kira ga kwamitin hakkin dan Adam na MDD da ya ci gaba da mai da hankali kan yanayin hakkin dan Adam a wadannan yankuna.

Mataimakiyar mai kula da harkokin hakkin dan Adam na MDD Kate Gilmore, ta yi bayani kan rahotanni guda shida game da yanayin hakkin dan Adam a yankunan da Isra'illa ta mallaka, inda aka gabatar da sabbin batutuwan keta dokokin jin kai da dokokin hakkin dan Adam da Isra'ila ta yi a yankunan, ciki har da tsare 'yan Falesdinu ba tare da izni ba da kuma habaka matsugunin Yahudawa da dai sauransu.

Kate Gilmore ta ce, 'yan Falesdinu kimanin miliyan 2 ba su da 'yancin kai saboda toshe yankin Gaza da Isra'ila ta yi, kuma a ko wace rana ana samar da wutar lantarki ne na tsawon sa'o'i 4 kacal, baya ga tsarin kiwon lafiyar yankin da ya kusan lalacewa gaba daya. Kana, amincewa da Jerusalem a matsayin babban birnin Isra'ila da Amurka ta yi, ta sake ta'azarra rikce-rikice tsakanin Falesdinu da Isra'ila.

A yayin taron, wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, dole ne a kiyaye ikon 'yan Falesdinu bisa dokoki yadda ya kamata. Kasar Sin ta kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su ci gaba da goyon bayan "daftarin kasashe biyu", domin dawo da Falesdinu da Isra'ila teburin sulhu cikin sauri, ta yadda za a warware matsalar cikin yanayi na adalci ta kowacce fuska. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China