Guterres ya bayyana hakan ne yau Litinin yayin da yake jawabi bikin bude zaman hukumar kare 'yancin dan-Adam ta MDD karo na 37.
Ya kuma yi kira ga kasashe mambobin hukumomin MDD da su kara goyon bayan matakan MDD game da kare hakkin dan-Adam. Yana mai cewa, da an mai da hankali ga batun kare hakkin dan-Adam a duniya cikin shekaru 20 din da suka gabata, da an kare miliyoyin rayukan jama'a a duniya. (Ibrahim)