A wannan rana da dare, fadar Kremlin ta fidda labari ta shafin intanet cewa, bisa gayyatar da kasar Amurka ta yiwa kasar Rasha, shugabannin kasashen biyu sun yi hira ta wayar tarho, inda suka yi tattaunawa kan yadda za su karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, ciki har da batutuwan tabbatar da zaman karko da kuma yaki da kungiyoyin ta'addanci a kasa da kasa. Haka kuma, bangarorin biyu sun jaddada cewa, ya kamata su hada kai domin hana yin gasar mallakar dunbun makamai.
Haka kuma, shugabannin biyu sun yarda da karfafa shawarwarin dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yi nazari kan batun ko za a iya gudanar da ganawar dake tsakaninsu, ko a'a.
Bugu da kari, sun yi tattaunawa kan batun Syria da na Ukraine, inda suka bayyana cewa, za su fitar da manufofi cikin sauri kan batutuwan. A sa'i daya kuma, sun nuna gamsuwa kan sassauta yanayi a zirin Koriya, sun jadadda cewa, ya kamata a ci gaba da daukar matakan diflomasiyya wajen warware wannan batu.
A yayin da suke shawarwarin, shugbannin biyu sun nuna sha'awarsu kan hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakaninsu, ciki har da hadin gwiwa a fannin makamashi.
Fadar Kremlin ta nuna cewa, babban makasudin yin shawarwarin dake tsakanin shugabannin biyu na wannan karo shi ne, warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokacin. (Maryam)