A wannan rana da dare, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fidda wata sanarwa cewa, babu shakka kasar Amurka tana da ikonta na katse huldar tattalin arzikin dake tsakaninta da kasar Rasha, amma kasar Rashar ita ma tana da nata ikon kan wannan fanni. Kuma takunkumin da kasar Amurkar ta kakabawa kasar Rasha ba zai yi wani tasiri ba ko kadan, sai dai ma ya haddasa hasara ga kamfanonin kasar Amurkan. (Maryam)