Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron dandalin da aka bude jiya a nan birnin Beijing, ya ce yana fatan kasar Sin za ta karfafa hadin kai tare da sauran kasashe a fannin kare hakkin bil adama.
Za dai a rika shirya dandalin ne a kowace shekara, ta yadda wakilan kasashe masu tasowa za su rika taruwa a Beijing don ba da shawarwari a wannan fannin. (Bilkisu)