in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron dandalin SSHRF
2017-12-08 16:49:23 cri

A yau Jumma'a ne aka rufe taron farko, na dandalin kare hakkin dan Adam tsakanin kasar Sin da kasashen masu tasowa wato SSHRF a nan birnin Beijing.

Taron wanda aka shafe kwanaki biyu ana gudanarwa ya samu halartar wakilai fiye da 300 daga kasashe da kungiyoyin duniya kimanin 70, inda suka tattauna kan ci gaban ayyukan kare hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa da na duniya, daga bisani kuma aka zartas da sanarwar Beijing.

Cikin sanarwar, an bayyana cewa, hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, wata muhimmiyar hanya ce ta ci gaban kasashen, da kuma aikin kare hakkin dan Adam na sassan. Sanarwar ta nuna cewa ya kamata kasashen su hada kansu a wannan fanni bisa ka'idojin kwazo tare, da sauke nauyin da ke wuyansu, da taimakawa juna don cimma nasara gaba daya, ta yadda za a iya ba da tabbaci sosai ga aikin kare hakkin dan Adam.

Bugu da kari, sanarwar ta bukaci sassan kasa da kasa, su kara goyon bayan saurin bunkasuwar kasashe masu tasowa, da kyautata aikinsu a fannin ba da tabbaci ga hakkin dan Adam, bisa ka'idojin samun daidaito, da kai zuciya nesa, da samar da amfani ga jama'a, kana da samun dauwamammen ci gaba.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China