Majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayar da takardar bayani kan ci gaban aikin kare hakkin bil Adama a kasar
Ofishin kula da harkokin labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin a yau Jumma'a ta kaddamar da takardar bayani mai taken sabon ci gaban aikin samar da dokokin kare hakkin bil Adama a kasar Sin.
Takardar ta ce, cikin shekaru da dama da suka wuce, kasar Sin ta tsaya kan manufar tafiyar da harkokin kasa bisa doka, a wani kokari na mayar da kasar matsayin wadda ke gudanar da harkokinta bisa doka, kuma ta yi ta samun ci gaba ta fannin kiyaye hakkin bil Adama bisa dokoki.(Lubabatu)