in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan gudun hijirar kasar Habasha kimanin dubu 250 sun koma gidajensu
2018-03-11 14:14:35 cri
Jiya Asabar, kwamitin kula da afkuwar bala'u na kasar Habasha ya fidda wata sanarwa cewa, 'yan gudun hijirar kasar kimanin dubu 250 wadanda suka rasa gidajensu sakamakon rikici sun riga sun koma gidajensu a yankunan kasar dake tsakanin jihar Oromiyaa da jihar Somali na kasar.

Wani jami'in kwamitin ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, mutane dubu 86 daga cikin wadannan 'yan gudun hijirar su dubu 250 sun riga sun samu gidajen kwana. Sa'an nan, a halin yanzu, gwamnatin kasar Habasha ta dukufa wajen dawo da sauran 'yan gudun hijirar kimanin dubu dari 6 gidajensu.

Haka zalika, jami'in kwamitin ya bayyana cewa, a watan Fabrairu na bana, jami'ai da shugabannin kabilu na jihar Oromiyaa da jihar Somali sun yi tattaunawa kan yadda za a warware sabanin dake tsakanin al'ummomin jihohin biyu, lamarin da ya ba da gudummawa kan dawowar 'yan gudun hijirar gidajensu.

An sha fama da sabani a tsakanin jihohin biyu kan batun shata kan iyakoki tsakaninsu. A shekarar 2004, al'ummomin jihohin biyu sun kada kuri'u domin sake shata kan iyakoki a yankunan biyu, amma dukkanninsu suna zargin junansu da gaza aiwatar da sakamakon yadda ya kamata. A watan Maris na shekarar da ta gabata, gwamnonin jihohin biyu sun kulla yarjejeniyar warware sabanin dake tsakanin jihohin biyu, amma yarjejeniyar ba ta iya shimfida kwanciyar hankali ba, sai samun karuwar rikice-rikice ake yi a yankunan dake tsakanin jihohin biyu tsakanin watan Satumba da Disamba na shekarar da ta gabata, lamarin da ya haddasa mutane masu dimbin yawa barin gidajensu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China