in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar tsaron kasar Habasha ta bukaci 'yan kasar su mutunta dokar-ta-bacin da aka kafa a kasar
2018-02-18 13:06:14 cri
Majalisar tabbatar da al'amuran tsaro ta kasar Habasha (ENSC) ta bukaci al'ummar kasar da su mutunta dokar ta-bacin da aka kafa wanda ta fara aiki tun daga ranar Jumma'ar da ta gabata a kasar.

Majalisar ministocin kasar ce ta ayyana dokar ta-bacin, tana mai cewa, ta yi hakan ne domin kare kundin tsarin mulkin kasar, da ba da kariya ga al'ummar kasar, da dukiyoyinsu daga fuskantar barazanar tashin hankalin dake wanzuwa a wasu sassan kasar a halin yanzu.

Siraj Fegessa, ministan tsaron Habasha, ya shedawa kafafen yada labaran kasar cewa, dokar ta-bacin da aka kafa za ta shafe tsawon watanni 6 ne, kuma dukkannin jami'an tsaron kasar za su yi aiki tare don tabbatar da ganin dokar tana aiki yadda ya kamata.

Kasar ta biyu mafi yawan jama'a a Afrika ta sha fuskantar dokar ta-baci har na tsawon watanni 10 tun daga watan Oktoban shekarar 2016, biyowa bayan matakin da majalisar dokokin kasar Habashan ta dauka na kara wa'adin watanni 4 daga cikin watanni shidan da aka sanya tun da farko na dokar-ta-bacin.

A cewar Fegessa, dokar-ta-bacin da aka kafa na watanni 10 a kasar ta yi matukar tasiri wajen lafawar tashin hankalin da ya barke a kasar ta gabashin Afrika musamman a cikin shekarar 2016 da 2017.

Fegessa ya nanata cewa za'a cigaba da tsawaita wa'adin dokar-ta-bacin muddin al'amura ba su daidaita ba a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China