in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar mai mulki a Habasha za ta yiwa 'yan adawa karin haske game da dokar yaki da ta'addanci
2018-01-12 10:48:20 cri
Jam'iyyun siyasa a kasar Habasha wadanda ke neman a cimma matsaya game da dokar yaki da ta'addanci a kasar sun amince za su saurari bahasi daga jam'iyyar dake mulkin kasar game da bukatar da suka gabatar mata.

Dama dai gamayyar jam'iyyun adawar kasar sun gabatarwa jam'iyya mai mulkin kasar bukatar sauya fasalin dokar, suna masu bayyana cewa, dokar ta ci karo da kundin tsarin mulkin kasar har ma da dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.

Haka zalika, jam'iyyun sun bukaci a fayyace musu yadda dokar take, kana sun bukaci a yi musu karin haske game da cigaban da aka samu a kokarin sakin wasu daga cikin fursunonin siyasar kasar.

Firaministan kasar Habashan Hailemariam Desalegn, tare da manyan shugabannin jam'iyyun siyasar kasar 4 na jam'iyyar EPRDF mai mulkin kasar, a kwanan nan suka bada sanarwar cewa, gwamnatin kasar Habashan zata janye tuhumar da ake yiwa fursunonin siyasar kasar kuma za'a sake su.

Desalegn, ya bayyana cewa, wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da hadin kan kasar, da sake gina kasa, da kuma bada damar tattaunawa a tsakanin al'ummomin kasar Habashan, kana gwamnatin kasar zata rufe cibiyar nan data yi kaurin suna wajen garkame mutane ta Maekelawi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China