in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Habasha ta kama mutane 107 bisa zarginsu da hannu wajen tada rikice-rikice tsakanin kabilun kasar
2018-01-06 13:19:43 cri
Jiya Jumma'a, kwamitin 'yan sandan tarayyar Habasha ya gabatar da wani rahoto game da rikice-rikicen a tsakanin kabilu daban daban a sassan kasar ga majalisar dokokin kasar ta Habasha, inda ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Habasha ta kama mutane 107 wadanda suke da hannu wajen ruruta wutar rikice-rikicen a tsakanin kabilu daban daban na kasar. Haka kuma, a cikin wadannan mutane 107, 98 daga cikinsu sun zo ne daga jihar Oromia, yayin da 9 daga cikinsu sun zo daga jihar Somali.

Jihar Oromia da jihar Somali suna kudu maso gabashin kasar Habasha, kuma fadin jihohin biyu sun kasance matsayi na daya da kuma matsayi na biyu a kasar. Kuma galibin mutane da suke zama a jihohin biyu su ne, 'yan kabilar Oromo da 'yan kabilar Somali, haka kuma, layin da aka kafa a tsakanin jihohin biyu yana da tsayi kwarai da gaske.

Cikin shekaru 20 da suka gataba, an yi ta samun tashin hankali a tsakanin mutanen jihohin biyu domin sabanin dake tsakaninsu kan batutuwan dake shafar yankin iyaka dake tsakanin jihohin biyu.

Haka kuma, tun daga watan Satumba na shekarar 2017, ya zuwa yanzu, rikice-rikicen da suka barke tsakanin mutanen jihohin biyu sun haddasa mutuwar mutane da dama, yayin da mutane sama da dubu dari 9 suka rasa gidajensu.

Haka zalika, bisa bayanin da kwamitin 'yan sandan tarayyar Habasha ya yi, an ce, bayan aukuwar rikice-rikice a tsakanin mutanen jihohin biyu, gwamnatin kasar ba ta dauki matakai cikin sauri da kuma yadda ya kamata ba, lamarin da ya haddasa tabarbarewar yanayi a yankin, har ma yara wadanda suke zaune a yankin iyaka dake tsakanin jihohin biyu ba su iya shiga makaranta kamar yadda ya kamata ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China