Bayan samun goron gayyata daga jam'iyyar (EPRDF) mai mulkin kasar Habasha, tawagar wakilan na kasar Sin karkashin jagorancin Wang Xiaohui, mataimakin shugaban sashen yada labarai na kwamitin tsakiya na jam'iyyar CPC, sun kai ziyarar aikin ne zuwa kasar ta gabashin Afrika tsakanin ranakun 22-24 ga watan Janairu. Wang, ya halarci taron tattaunawa wanda aka gudanar a kwalejin nazarin shugabanci ta Meles Zenawi da kuma jami'ar Addis Ababa, inda aka tattauna game da muhimman batutuwan da suka shafi babban taron na CPC karo 19.
Jam'iyyar ta EPRDF, ta nuna sha'awa matuka na kara karfafa yin hadin gwiwa ta kut-da-kut da CPC da kuma yin musayar kwarewa wajen tafiyar da sha'anin jam'iyyar da shugabancin kasar baki daya.