in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha da Sin sun alkawarta kara bunkasa hadin gwiwa a muhimman fannoni
2018-01-29 20:09:11 cri
Habasha da kasar Sin sun alkawarta karfafa hadin gwiwa a fannin inganta alakar dake tsakanin su a sassa daban daban da suke cin gajiyar su.

Kasashen biyu sun jaddada wannan aniya ne, yayin wani zama da ministan harkokin wajen kasar Habasha Workneh Gebeyehu yayi da mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, a gefen taron kolin shugabannin kungiyar hadin kan Afirka ta AU karo na 30 dake gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Tuni dai kasar Habasha ta bayyana alakar ta da kasar Sin a matsayin daya daga mafiya muhimmanci a harkokin ta na diflomasiyya da sauran sassa.

A wani ci gaban kuma, ministan harkokin sufuri na kasar ta Habasha Ahmed Shide, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, hadin gwiwar kasar sa da Sin ya haifar da babbar nasara ga Habasha a fannonin cinikayya da musaya tsakanin al'ummun kasashen biyu.

Sin ita ce abokiyar cinikayya mafi girma ga Habasha, tana kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa zuba jari a Habasha, da hada hadar cinikayya da kuma fannin diflomasiyya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China