in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU zata goyi bayan ajandar kyautata shugabancin kasar Habasha
2018-02-22 10:26:45 cri
Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya jaddada aniyar kungiyar wajen goyon bayan shirin inganta sha'anin shugabanci a kasar Habasha.

Mahamat ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawa da firaministan kasar Habashan Hailemariam Desalegn da yammacin ranar Laraba, a game da dambarwar siyasar daya dabaibaye kasar dama sauran batutuwa da suka shafi kasar ta gabashin Afrika, kamar yadda wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar da hakan.

Mahamat, ya lura da irin muhimmiyar rawar da kasar Habashan ke takawa game da cigaban kungiyar AU, da kuma kokarin da take yi wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, yace kungiyar AU a shirye take ta taimakawa ajandar kawo sauyi a kasar Habashan, kuma zata yi amfani da dukkan dabarunta wajen shawo kan kalubalolin da kasar ke fuskanta a fannonin rashin ayyukan yi a tsakanin matasan kasar da fadada tsarin siyasar kasar.

Shugaban na AU ya bayyana kwarin gwiwarsa game da matakan da Habasha ke dauka na warware matsalar rikicin cikin gidan kasar. Kana ya yabawa gwamnatin kasar Habashan game da karin hasken da ta yiwa jami'an diplomasiyya a kasar dangane da rikicin siyasar da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Ganawar bangarorin biyu ta zo ne a daidai lokacin da kasar Habashan ke fuskantar rikicin kabilanci, lamarin da ya haddasa firaiministan kasar Desalegn yin murabus daga mukaminsa a makon jiya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China