Jiya Asabar, a yayin da tawagar wakilan jama'ar birnin Chongqing ta halarci taron tattaunawa kan rahoton gwamnati, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, aikin gina yanayin siyasa mai adalci da tsari wanda babu cin hanci da karbar rashawa shi ne muhimmiyar bukatar da ake da shi na kiyaye ikon mulkin kasa na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS, kana, muhimmin abu ne wajen inganta bunkasuwar ayyukan JKS da kuma kyautata yanayin siyasar JKS, ta yadda za a iya bada tabbaci wajen cimma burin yin kwaskwarima a kasar Sin da kuma neman ci gaba.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata a mai da hankali kan ayyuka na wasu muhimman shugabannin kasar, domin su zama abin koyi da kuma yin jagoranci ga al'ummomin kasar. (Maryam)