in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin da Sin ta kashe kan tsaron kasa ba shi da yawa, in ji wakilin taron NPC
2018-03-09 09:57:11 cri

Wakilin babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC kuma mataimakin shugaban cibiyar nazari kan aikin soja ta kasar Sin He Lei ya ce, kudin da kasar Sin take kashewa kan aikin tsaron kasa ba shi da yawa, idan aka kwatanta adadinsu da sauran kasashen duniya, za a lura cewa, kudin da kasar Sin ta kashe kan aikin ya fi kankanta. Ya ce ana iya gano hakan ne daga fannoni uku da suka hada da kason aikin dake cikin GDP na kasar da adadin kudin da kowanen soji ya kashe da kuma adadin kudin da kowane dan kasar ya kashe.

Rahoton kasafin kudi da ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta gabatar yayin babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar a ranar 5 ga wata, ya yi nuni da cewa, a shekarar 2018 da muke ciki, kudin da kasar za ta kashe kan aikin tsaron kasa zai karu da kaso 8.1 bisa dari, adadin da zai kai kudin Sin yuan biliyan 1106 da miliyan 951.

He Lei ya bayyana cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin ta na kayyade kudin da take kashewa kan aikin tsaron kasa, inda take amfani da su a fannoni biyar, wato mayar da kudin da aka kashe a cikin 'yan shekarun da suka gabata bisa dalilin karancin kudin tsaron kasa, da samar da makamai, da kyautata rayuwar sojoji da biyan bukatun atisayen aikin soja, tare kuma da biyan bukatun da ake da su ta fuskar yin gyaran fuska ga rundunar sojin kasar.

He Lei ya jaddada cewa, duk da cewa kasar Sin tana samun ci gaba cikin sauri, ba zai yiwu ta nuna karfi ko girma, balle ta yi gogayya da sauran kasashen duniya wajen aikin soja ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China