Ba da gudummawa ga harkokin cikin gida, nauyi ne da ya shafi harkokin diflomasiyya na kasar Sin
Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, har yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa, kana ba da gudummawa ga harkokin cikin gida, nauyi ne da ya shafi harkokin diflomasiyya na kasar Sin bisa halayyar musamman na Sin. A shekarar da ake ciki, ma'aikatar harkokin wajen kasar za ta yi aikin yayyata sabon yanki na Xiong An ga duniya baki daya.
Mr. Wang ya fadi haka ne a yau da safe a yayin wani taron manema labaru da aka shirya yayin cikakken zaman farko na babban taron wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 da ake yi a nan Beijing.
Wang Yi ya kara da cewa, ma'aikatarsa za ta kara mai da hankali kan aikin kawar da talauci, kuma za ta ba da gudummawarta kamar yadda ya kamata wajen kokarin samun nasarar kawar da talauci baki daya a kasar. (Sanusi Chen)