in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan ciniki: an samu dandazon masu sha'awar halartar bikin baje kolin kasar Sin
2018-03-11 13:08:00 cri
Ministan cinikin kasar Sin Zhong Shan ya bayyana a yau Lahadi cewa, wajen da aka kebe don gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kasar Sin ya samu sama da kashi 20 bisa 100 na masu sha'awar halartar bikin wadanda tuni suka kama wuraren, bikin za'a gudanar ne a birnin Shanghai a watan Nuwamba.

Sama da kamfanoni 120 daga kasashe da yankuna daban daban na duniya ne suka mika takardun neman izinin halartar bikin baje kolin, in ji mista Zhong a lokacin da yake jawabi a taron manema labarai a wajen taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13 dake gudana a halin yanzu.

Ya ce sama da 'yan kasuwa dubu 150 daga sassan duniya daban daban ne ake sa ran za su halarci bikin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China