Yanzu kasar Sin tana kara habaka tasirinta a fadin duniya, a don haka wasu suke zargin cewa, kasar tana kawo barazana ga sauran kasashen duniya, sai dai a yayin taron ganawa da manema labarai na farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 da aka gudanar a safiyar yau, ministan harkokin wajen kasar ta Sin Wang Yi ya karyata wannan ra'ayin.
Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen karuwar tattalin arzikin duniya da kuma yaki da talauci, kana tana ba da karin gudummowa wajen kiyaye zaman lafiya a fadin duniya, ban da haka kuma, ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, domin gudanar da harkokin duniya tare da sauran kasashe yadda ya kamata.(Jamila)