Kasar Sin ta bayyana kudurinta na ganin kotunan dake fadin kasar sun yiwa jama'a adalci a duk kan kararrakin da suka shigar a gabansu, kamar yadda wani rahoton aiki da kotun kolin al'umma ta kasar Sin ta fitar a yau Jumma'a.
A cewar rahoton, daga shekarar 2013 zuwa 2017, an gabatarwa kotun kolin al'ummar kasar kararraki 82,383 inda ta yanke hukunci kan kararraki 79,682, wato kaso 60.6 cikin dari na wadanda aka gabatar, sai kuma kaso 58.8 cikin 100 na wadanda aka yanke hukunci. Adadin da ya dara na shekaru biyar da suka gabata.
A yau ne dai babban mai shari'a Zhou Qiang ya gabatar da wannan rahoto a zaman farko na ganawar majalisar wakilai karo na 13 dake gudana a birnin Beijing, ya kuma lashi takwabin kare ikon kundin tsarin mulki tare kuma da yakar duk wani yunkuri na keta kundin tsarin mulkin.
Zhou Qiang ya kuma jaddada cewa, kotun kolin al'umma za ta yi kokarin tunkarar duk wasu matsaloli da kalubale yayin da ake aiwatar da gyare-gyare a kotunan kasar. (Ibrahim)