A safiyar yau Alhamis, cibiyar labarai ta taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasa ta 13 ta kira taron manema labarai na ministan harkokin wajen kasar Sin, inda Mr. Wang ya bayyana cewa, manyan ayyukan diflomasiyya guda hudu da kasar Sin za ta yi a shekarar bana su ne, taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar kasashen Asiya na Bo'ao da za a yi a lardin Hainan a watan Afrilu mai zuwa, inda za a yi nazari kan fasahohin kasar Sin wajen aiwatar da harkokin bude kofa ga waje, da nuna kyakkyawar makoma ta zurfafa ayyukan yin kwaskwarima da kara bude kofa ga waje.
Sa'an nan, za a yi taron kolin kunigyar hadin gwiwa ta Shanghai a watan Yuni a birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin.
A watan Satumba kuma, za a yi taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a birnin Beijing, inda za a mai da hankali kan yadda za a aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", domin samar da sabbin damammaki ga bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare.
A karshe, a watan Disamba na shekarar bana, za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigar da su daga ketare na kasa da kasa a birnin Shanghai karo na farko, inda kasar Sin za ta nuna maraba ga kasa da kasa, da su zo kasar Sin domin yin musayar ra'ayoyi kan fasahohin neman ci gaba, da kuma yin amfani da sabbin damammakin neman bunkasuwa a sabon zamani cikin hadin gwiwa. (Maryam)