in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: Shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da damammaki ga kasashen dake cikinta
2018-03-07 20:37:55 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, shawarar Ziri daya da haya daya ta samar da sabbin damammaki da makoma ga kasashen dake cikin shawarar.

Geng Shuang ya bayyana hakan ne yau Laraba a nan birnin Beijing yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai da aka saba game da rahoton da cibiyar raya kasashe ta duniya dake Washington na kasar Amurka ta wallafa, wanda ya ce shawarar Ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta bullo da ita, tana iya kara hadarin basussuka ga kasashe kamar Pakistan da Montenegoro da Djibouti.

Jami'in na kasar Sin ya ce, da dama daga cikin kasashen dake cikin wannan shawara kasashe ne masu tasowa, wadanda suke bukatar kayayyakin more rayuwa, kuma wannan shawara ta kara samar da sabbin damammaki ga wadannan kasashe wajen inganta rayuwar al'ummominsu har ma su raya kasashensu.

Ya ce shawarar, ta zama wata babbar kafar hadin gwiwar kasa da kasa kana dandalin mafi shahara da ya taimakawa al'umma a duniya. A don haka ta yaya zai iya cimma wannan nasara, idan har yana tattare da hadari kamar yadda wasu ke fada?(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China