Xi Jinping na fatan yankin Mongolia na gida zai yi kokarin raya tattalin arziki mai inganci tare da kawar da talauci daga yankin
Da yammacin ranar 5 ga watan Maris, wato ranar da aka kaddamar da zagayen farko na babban taron wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya halarci taron tattaunawa kan rahoton aikin gwamnati da aka gabatar wanda kungiyar wakilan yankin Mongolia na gida ya shirya, inda Xi Jinping ya ba da shawarar raya yankin Mongolia na gida, tare da neman jami'ai da al'ummomin yankin su yi namijin kokari da kuma kara hada kan kabilu daban daban domin bunkasa tattalin arziki mai inganci, da samun sakamako na a zo a gani wajen kawar da talauci daga yankin. Bugu da kari, yana fatan kabilu daban daban da suke zaune a yankin, za su kara hada kai domin tabbatar da tsaron yankin dake kan iyakar kasa da kasa dake arewacin kasar Sin. (Sanusi Chen)