in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu nasara kan yaki da talauci
2018-03-07 20:34:20 cri
A yau Laraba ne, mataimakin shugaban hukumar yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin Liu Yongfu ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a shekaru 5 da suka gabata, yawan matalauta a kasar Sin ya ragu da miliyan 68 da dubu 530, wannan wata babbar nasara ce kan yaki da talauci da kasar Sin ta samu a tarihi.

Mr Liu ya yi bayani cewa, Sin ta kuma zuba jari ga aikin yaki da talauci, da kyautata ayyukan more rayuwa, da samar da hidimar yau da kullum a yankuna masu fama da talauci. Kana an bunkasa sana'o'in musamman a yankuna masu talauci, baya ga kyautata muhallin halittu.

Bisa burin da kasar Sin ta tsara, tana fatan nan da shekarar 2020 za ta kawar da talauci bisa ma'aunin kasar Sin. Mr Liu ya bayyana cewa, Sin ta yi imani za ta cimma wannan buri. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China