in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi: Tsarin jam'iyyun kasar Sin babbar gudunmawa ce ga wayewar kan bil adama ta fuskar siyasa
2018-03-08 10:15:39 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ayyana tsarin hadin kan jam'iyyu da tsarin tuntubar juna wanda jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ke jagoranta babbar gudumawa ce dake samar da wayewar kai ga bil adama ta fuskar siyasa.

Wannan "wani sabon tsarin jam'iyyu ne dake samun tagomashi wanda kasar Sin ta bullo da shi", in ji shugaba Xi, kana babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin tsakiya na dakarun tsaron kasar Sin, ya furta hakan ne a lokacin da ya halarci taron tattaunawa da jiga-jigan siyasa da suka fito daga gamayyar jam'iyyun kasar Sin wato China Democratic League da kuma jam'iyyar China Zhi Gong Party, wannan ya kunshi mutanen da ba su da alaka da wata jam'iyyar siyasa da kuma Sinawana da suka dawo daga kasashen ketare, inda suka gana a zaman farko karo na 13 na taron kwamitin ba da shawara kan al'amurran siyasar kasar Sin (CPPCC).

Ya ce a halin yanzu, an jingine tsoron tsarin siyasa da ake amfani da shi mai cike da rauni, wanda wasu jam'iyyun siyasa, da wasu shafaffu da mai, da kungiyoyin addinai, suke raba kan al'umma.

Xi ya ce, bin tsarin shugabancin jam'iyyar CPC ba ya nufin yin watsi da tsarin demokaradiyya ba ne.

A maimakon hakan, JKS na kokarin kafa wani tsarin demokaradiyya mai fadi kuma mai matukar inganci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China