Bugu da kari, shugaba Xi ya ce, ya kamata lardin Guangdong ya kama muhimmiyar dama ta raya yankunan Guangdong, Hong Kong da Macau, da kuma yin hadin gwiwa da bangarorin Hong Kong da Macau wajen ciyar da ayyukan da abin ya shafa gaba, ta yadda za a kafa wani yanki na birane masu ci gaba a duniya.
A yayin taron, shugaba Xi ya saurari jawabin da wakilan lardin Guangdong suka gabatar, inda ya kuma yi shawarwari tare da su. Wannan shi ne karo na biyu da Xi Jinping ya halarci taron wakilan na lardin Gongdong, bayan na shekarar 2014, wanda shi ne karo na farko da ya halarci taron na wakilan lardin Guangdong.
Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 40 da kasar Sin ta fara bude kofa ga waje, kana, lardin Guangdong ya zama lardin dake kan gaba wajen aiwatar da harkokin bude kofa ga waje, shi ya sa, jawabin da shugaba Xi ya gabatar wa tawagar wakilan lardin Guangdong ya janyo hankulan bangarori daban daban kwarai da gaske. (Maryam)