Haka kuma ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima kan tsarin karbar kudin haraji domin taimakawa bunkasar sana'o'i daban daban a kasar. A sa'i daya kuma, za a yi kwaskwarima kan tsarin haraji kan kudin shiga da mutanen kasar ke samu, tare da karfafa taimakon da za a ba kanana, da matsakaitan kamfanonin kasar.
Bugu da kari, ya ce, bisa kididdigar da aka yi, gaba daya, za a rage haraji na kudin yuan biliyan dari 8 cikin shekarar 2018, bayan fara aiwatar da manufofin rage haraji a kasar.
Har ila yau, za a dadaita tsarin asusun gwamnatocin kasar da kuma tsarin karbar kudi kan harkokin gudanarwa da ba da hidima da dai sauransu, inda gaba daya za a rage kudin yuan biliyan dari 3 a wadannan fannoni. (Maryam)