in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da yin kwaskwarima a kasar Sin domin kyautata zaman rayuwar al'umma, in ji firaministan kasar
2018-03-07 10:14:40 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, ya kamata a ci gaba da yin kwaskwarima a kasar, domin karfafa yanayin bunkasar kasa, inda ya ce, cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta cimma babban sakamako wajen neman ci gaba.

Li Keqiang ya bayyana haka ne da safiyar jiya, lokacin da yake jawabi ga taron nazari kan rahoton gwamnati na tawagar wakilan yankin Guangxi mai cin gashin kansa.

Firaministan ya kuma jaddada cewa, dole ne a nemi ci gaba bisa bukatun al'ummomin kasa, domin babban burin yin kwaskwarima a kasar Sin shi ne, kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa.

Ya kara da cewa, ya kamata gwamnatocin yankunan kasar su kara samar da kudade wajen kiyayewa da kyautata zaman rayuwar al'ummominsu, tare da mai da hankali kan taimakawa wurare masu fama da talauci, da kuma samarwa al'ummomin wuraren damarmakin neman ci gaba da kansu, kamar habaka sana'o'in da za su dace da yanayin wuraren da tsara wasu shirye-shiryen neman raya kansu da kuma samar musu taimakon kudade da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China