Yau Talata, mataimakin shugaban hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Ning Jizhe ya bayyana a yayin taron manema labarai da cibiyar labarai na taron majalisar wakilan jama'ar kasa ta Sin ta kira cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata yanayin gudanar da harkokin ciniki a wurare daban daban dake fadin kasar, domin samar da sauki a harkokin cinikayya ga kamfanoni da al'ummomin kasar.
Haka kuma, ya ce, a bana za a rage samar da yuan biliyan dari 8 na haraji ga kamfanoni da al'ummomin kasar. (Maryam)