Dan majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin(CPPCC) kana babban mai tsara harkokin zirga-zirgar sararin samaniya a kasar, Zhou Jianping a jiya Lahadi ya bayyana cewa, masu nazarin kimiyya na kasar Sin tuni sun fara nazarin samfurin sassan tashar sararin samaniya, sassan da suka hada da wani babban kumbo da kuma wasu kumbuna biyu na gudanar da ayyukan gwaji.
Jami'in ya ce, kasar Sin tana shirin harba babban kumbo na tashar a shekarar 2020, don gwada muhimman fasahohin da suka shafi tashar. Daga baya, za ta harba sauran kumbuna biyu na gwaji, don a hada su da babban kumbo.(Lubabatu)