Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito rahotanni game da wasu muhimman sassan dake cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, inda ake ganin cewa, habaka tattalin arziki ta hanyar da ta dace zai taka muhimmiyar rawa yayin da kasar Sin ke kokarin neman cimma manufofi ya zuwa lokacin da za'a yi bukukuwa 2 na cika shekaru 100, wato, kammala samar da al'umma mai matsakaicin ci gaba ta kowace fuska, ya zuwa lokacin da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta yi bikin cika shekaru dari a shekarar 2021, tare da mayar da kasar Sin zuwa ta zamani, wadda ta samu nasarori a fannonin karfin mulki da demokradiyya da inganta al'adu da kwanciyar hankali, a lokacin da Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin za ta yi bikin cika shekaru dari a shekarar 2049.
Shi kuwa kamfanin AP na kasar Amurka ya maida hankali ne kan wasu matakan gwamnati dake kunshe cikin rahoton, ciki har da yin kwaskwarima ga tsarin samar da kayayyaki da gaggauta raya kasa ta fannin bunkasa sana'ar kere-kere, inda aka ce, kasar Sin za ta kara azama wajen habaka wasu sana'o'i, ciki har da fasahar sadarwa ta 5G, da injin jirgin sama, da kuma kera motoci masu amfani da sabon makamashi.(Murtala Zhang)