Yana ganin cewa, a bana, za a ci gaba da samun karuwar kashe kudi a duk fadin kasar Sin, sabo da bunkasuwar sabbin sana'o'i da sana'o'in ba da hidima na zamani, lamarin da zai ba da babbar gudummawa ta kashi 60 bisa dari ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, ana dukufa wajen tsara wasu manufofin da za su habaka harkokin zuba jari a fannoni daban daban a kasar, wadanda za su ba da gudummawar kashi daya bisa uku ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
A sa'i daya kuma, za a ci gaba da samun karuwa a fannin shiga da fitar da hajoji a tsakanin Sin da kasashen ketare, wanda shi ma zai ba da gudummawa ta kashi 8 zuwa 9 bisa dari ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. (Maryam)